✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa 

Har yanzu ba a san inda maharan suka kai alƙalin ba.

Wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Alƙalin Babbar Kotun Jihar Bayelsa, Ebiyerin Omukoro.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Asabar a unguwar Ekeki, kusa da babban titin Melford Okilo a Yenagoa, babban birnin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen sun isa a cikin mota ƙirar Hilux, sanye da baƙaƙen kaya.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, maharsn sun kutsa kai gidan cin abincin da alƙalin ke ciki kuma suka tilasta masa shiga motarsu.

Har zuwa yanzu, ba a san inda suka kai shi ba, kuma babu wani saƙo ko buƙatar kuɗin fansa daga masu garkuwar.

Hakazalika ba a san dalilin da ya sa suka sace shi ba.

Wannan ba shi ne karon farko da aka sace mutum a yankin ba, domin an je har gida an sace wani ɗan jarida mai suna Oyins Egrenbido.

Wasu hotuna da bidiyo da suka karaɗe shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka kama alƙalin tare da jefa shi cikin motar ƙirar Hilux.

Har yanzu Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da sace alƙalin.