Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wani mai suna Olukoye Olalekan hukuncin daurin shekaru 76 a kukuku saboda yada hotunan tsiraicin yara kanana da kuma aikata damfara.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Alexander Owoeye, ne ya yanke hukuncin ranar Alhamis, bayan ya samu mutumin da aikata laifukan da aka zarge shi da su.
- Rikicin Filato: An sake kashe mutum 17 a Mangu da Bokkos
- 2027: ‘Sai bayan babban taron APC Tinubu zai bayyana wanda za su yi takara tare’
An dai gurfanar da Olukoye ne a gaban kotun ana zarginsa da laifuka 18 da suke da alaka da yada hotunan tsiraicin yara kanana, damfara ta intanet, boye kudaden haram da kuma mallakar kadarori ta haramtacciyar hanya, wanda Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.
A cewar lauyar masu kara, Bilkisu Buhari-Bala, laifukan sun saba wa tanade-tanaden sassa na 23(1)(c) da 23(1)(f) na kundin laifukan intanet da kuma sassa na 18(3),16(2)(a),16(3),1(1)(a), da 1(2) na kundin hana almundahanar kudade.
Yayin shari’ar, lauyar ta EFCC ta shaida wa kotun cewa Olukoye ya bude wasu shafukan sada zumunta a dandalin sada zumunta irin su Snapchat da Instagram, wadanda ya rika amfani da su a matsayin mace daga jihar North Carolina ta Amurka.
Lauyar ta ce mutumin ya rika amfani da shafukan wajen damfarar mutane har ta kai ga ya mallaki wani gida, ta hanyar yin barazanar wallafa hotunan tsiraicin yara kanana a shafukan.
Da yake yanke shukunci, Mai Shari’a Alexander ya sami Olukoye da dukkan laifukan sannan ya yanke masa hukuncin jimillar daurin shekara 76 a gidan kaso.