Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000.
Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan neman bukatar janye karar da aka daukaka.
Bukatun dai na kunshe ne a cikin wasu kararraki masu lamba CV/395/M1/2025 da kuma CV/395/M2/2025, wadanda aka shigar a ranakun uku da kuma 25 ga watan Mayun 2025, wanda a cikinsu aka ambaci sunan Akpabio a matsayin mai daukaka kara.
- DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya
- Rikicin Filato: An sake kone gidaje 96 a Mangu
Wadanda ake kara kuma su ne Sanata Natasha da Magatakardar Majalisar Dokoki ta Kasa da Majalisar Dattawa da shugaban kwmaitin da’a, ladabtarwa da korafe-korafen jama’a na majalisar, Sanata Neda Imasuem.
Tun farko dai a cikin karar, Akpabio ya nemi kotun da ta kara masa lokacin da zai iya kalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke mai lamba FHC/ABJ/CS/384/2025, wanda ta yanke ranar 10 ga watan Maris 2025 bisa hujjar cewa akwai kura-kurai a cikinsa.
Sai dai da take yanke nata hukuncin, kotun ta ce ta amince da bukatar janye kararrakin guda biyu, kamar yadda mai kara ya bukata.
Sai dai ta ce ta ci mai karar tara Naira 100,000, wadanda za a ba wacce aka yi kara.