✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akpabio ya daukaka kara kan hukuncin mayar da Natasha kujerarta

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya daukaka kara a gaban kotu a Abuja yana kalubalantar umarnin mayar da dakatacciyar Sanata, Natasha Akpoti-Uduaghan kan kujerarta.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya daukaka kara a gaban kotu a Abuja yana kalubalantar umarnin mayar da dakatacciyar Sanata, Natasha Akpoti-Uduaghan kan kujerarta.

A ranar hudu ga watan Yuli ce dai Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin mayar da Sanata Natashar kan kujerarta inda ta ce hukuncin dakatarwar wata shidan da aka yi mata ya yi tsanani.

Kotun ta kuma ci tarar ita Sanata Natashar naira miliyan biyar kan wallafa wata wasikar zambo a kan Akpabio a shafinta na Facebook, duk da kotun a baya ta yi hani da hakan.

Sai dai a wata karar da Akpabio ya shigar ta hannun lauyoyinsa a gaban Kotun Daukaka kara da ke Abuja, ya bukaci ta jingine hukuncin kotun ta baya saboda ya ce batu ne na cikin gidan majalisar.

Ya kuma ce dukkan abubuwan da suka faru a zauren majalisar, ciki har da shawarwarinta da dakatar da mambobinta, na karkashin dokokin majalisa, kuma bai kamata a kai su gaban kotu ba.

Akpabio ya kuma zargi Natasha da gaggawar shigar da karar tun da farko a maimakon ta bari ta kamala bin dukkan matakan cikin gida da dokokin majalisar suka tanada, kamar yadda yake a Kundin Dokokin Majalisar na 2023, wanda aka yi wa gyaran fuska.

A watan Maris din da ya gabata ne majalisar karkashin Sanata Akpabio ta dakatar da Natsha bisa zarginta da nuna rashin da’a a, bayan ta zargi Akpabion da yunkurin cin zarafinta da kuma canza mata wurin zama a majalisar.