✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio

Babbr Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, kan Naira miliyan 50.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, kan Naira miliyan 50.

Kotun dai, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Chizoba Orji, ta kuma yi watsi da bukatar Gwamnatin Tarayya kan wacce ake karar cewa a kulle ta a kurkuku har zuwa lokacin yanke hukunci.

Mai Shari’ar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa ta hana wacce ake karar beli ba, inda ta ce akwai gamsassun hujjojin da ke nuna cewa a shirye take ta fuskanci shari’ar.

Sai dai baya ga Naira miliyan 50 din, kotun ta kuma umarci Sanata Natasha ta gabatar da wanda zai tsaya mata, wanda kuma dole ne ya kasance mutum mai kima kuma wanda yake da kadara a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kotun dai ta ce ta yi amfani da tanade-tanaden sashe na 36 ne na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kuma sashe na 163 da 165 na kundin manyan laifuffuka na 2015.

Daga nan ne sai kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 23 ga watan Satumban 2025.

Gwamnatin Tarayya ce dai ta gurfanar da Sanata Natasha tana zarginta da yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, karya wai suna so su kashe ta.

A cikin karar mai lamba CR/297/25, gwamnatin ta yi karar Natasha kan kalaman da ta yi yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Politics Today, a kwanakin baya.