Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe don yin wa’adi na biyu a 2027, duk da ƙoƙarin ’yan adawa na ƙalubalantarsa.
Yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa-baki da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) ta shirya a Abuja, Akpabio ya nuna ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulki.
- Sallah: Hadimin gwamnan Sakkwato ya bai wa magoya bayan APC kyautar N22m
- ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano
“Za mu dawo a 2027, da sunan Yesu, Amin,” in ji shi.
“Za mu yi wa jam’iyyarmu da Shugaban Ƙasa addu’a. Wa’adin mulkinsa na biyu ya tabbata.”
Liyafar, wacce gwamnonin APC, ’yan majalisa, da ministoci suka halarta, ta zama gangamin siyasa, inda shugabannin jam’iyyar suka jaddada nasarorin Tinubu.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce APC za ta ci gaba da mulki: “Yunƙurin ’yan adawa na ƙwace mulki daga hannun Tinubu ba zai yi nasara ba.
“Dole mu yi amfani da ‘wa’azin siyasa’ don nuna ci gaban da muka samu.”
Duk da cewa Tinubu bai sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a karo na biyu ba, shugabannin APC sun fara gangamin mara masa baya ta hanyar taruka da nuna goyon baya, yayin da ’yan adawa ke sukar hakan a matsayin kamfe.