✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC

Ganduje ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya sa ya ajiye shugabancin jam'iyyar.

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar.

Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.

Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya da ya ajiye muƙaminsa.

Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.

Lokacin da ya kwashe a matsayin shugaban jam’iyyar na cike da cece-kuce da suka.

Dalilin murabus ɗinsa

Ko da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin siyasa a cikin jam’iyyar ne suka tilasta masa ajiye muƙamisa.

Haka kuma, an danganta murabus ɗinsa da zarge-zargen almundahana da karkatar da kuɗaɗe.

Wasu ’ya’yan jam’iyyar sun koka cewa ofishinsa na tilasta musu biyan kuɗi da yawa, musamman masu neman tikitin takara a Abuja.

Tasirin murabus ɗinsa ga jam’iyyar APC

Murabus ɗin Ganduje babban sauyi ne ga shugabancin jam’iyyar APC.

Yanzu haka, mutane da dama suna jiran su ji yadda jam’iyyar za ta shawo kan wannan lamari.

Har yanzu jam’iyyar APC ba ta fitar da wata sanarwa kan murabus ɗinsa ba.

Matsalolin da suka shafi Ganduje kan shugabancin jam’iyyar

A farkon shekarar 2024, wata kotu a Jihar Kano ta hana Ganduje ci gaba da kiran kansa da ɗan jam’iyyar APC, bayan wasu shugabannin jam’iyyar sun shigar da ƙara a kansa.

Daga baya kuma, wata kotu a Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu ke yi don a tsige shi daga shugabancin jam’iyyar.

Zamanin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar cike yake da rikice-rikice, kuma murabus ɗinsa yanzu zai sanya dasa ayar tambayoyi domin neman wasu amsoshi.