✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici

Sakataren ya ce an ɗauki matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata.

Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata.

Gwamna Umaru Bago ya amince da rufe jami’ar nan take, kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyi.

“Lafiyar kowa, musamman ɗalibai da malamai, na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Jihar Neja,” in ji sanarwar.

“Mun yi matuƙar baƙin ciki da abin da ya faru, kuma muna ɗaukar matakan gaggawa don magance lamarin.”

Gwamnatin ta roƙi ɗalibai, malamai da ma’aikatan jami’ar su kwantar da hankalinsu, kuma su kasance masu lura, su kuma yi aiki tare da jami’an tsaro a wannan lokaci.

Haka kuma gwamnatin ta tabbatar da cewa tana ɗaukar matakai domin wanzar da zaman lafiya.

Ta ce duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

“Za mu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da kuma tabbatar da doka da oda a faɗin Jihar Neja,” in ji sanarwar.