Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanya wa sabuwar gadar sama da aka kammala a Lafia, Babban Birnin Jihar, sunan Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da aikin a Lafia.
- ’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya
- An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano
Ya ce an gina gadar bisa tsarin Shugaba Tinubu, kuma an kammala aikin ne ba tare da ciyo bashi ba, sakamakon inganta amfani da kuɗin gwamnati.
Sabuwar gadar mai tsawon kilomita ɗaya, wadda ke da gadar sama da ƙasa, na ɗauke da sunan ‘Bola Tinubu Exchange Road’.
A wajen buɗe aikin, Shugaba Tinubu ya gode wa Gwamna Sule bisa jajircewarsa wajen aiwatar da ayyukan da ke taimaka wa rayuwar al’umma.
Haka kuma, ya nuna farin cikinsa da irin tarbar da ya samu daga mutanen Nasarawa.
Sannan ya yi kira a gare su da su ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya.