Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya karɓi ragamar shugabancin daga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
An sanar da hakan ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 67 da aka gudanar a Abuja.
- An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna
- ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa
Shugaba Tinubu, wanda ya yi wa’adin shugabancin ƙungiyar sau biyu tun daga shekarar 2023, ya bayyana cewa shugabancin ECOWAS babban abu ne a rayuwarsa.
Ya ce: “Yayin da nake miƙa ragamar shugabanci ga abokina kuma ɗan uwana, Shugaba Julius Maada Bio, ina mai gamsuwa da fatan alheri ga makomar Yammacin Afirka.”
Ya ƙara da cewa wajibi ne ƙasashen yankin su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban dimokuraɗiyya da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.
“Mu ƙara inganta haɗin kai, mu mutunta ƙa’idojin diflomasiyya, sannan mu tabbatar da ci gaba wanda zai haɗa kowa da kowa musamman matasa, mata da waɗanda ke cikin mawuyacin hali,” in ji Tinubu.
A jawabinsa na karɓar shugabanci, Shugaba Bio ya gode wa Tinubu bisa jagoranci mai cike da hangen nesa da kyakkyawan fata.
Ya ce: “Shugabancinka a ECOWAS ya nuna jajircewa wajen ƙarfafa tattaunawar yankin, farfaɗo da tattalin arziƙi da wanzar da zaman lafiya.
“Na ji kaina a matsayin mai ɗaukar wannan nauyi domin ci gaba daga inda ka tsaya.”
Shugaba Bio ya bayyana cewa akwai buƙatar ECOWAS ta ƙara dagewa wajen kare dimokuraɗiyya, inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziƙi.
“Dole mu sake fasalin ECOWAS ta yadda za ta zama mai gaskiya, inganci da amsa buƙatun al’ummarta,” in ji shi.
Ya kuma bayyana matsalolin da yankin ke fuskanta kamar ta’addanci, taɓarɓarewar siyasa da matsin tattalin arziki.
Ya ce: “Fagen dimokuraɗiyya yana fuskantar ƙalubale a sassa daban-daban na yankin. A wasu ƙasashe, tsarin mulki ya rikiɗe.
“Amma matasa na faɗin Yammacin Afirka na buƙatar ba kawai zaɓe ba, har ma da gaskiya, da ba su damar shiga cikin tafiyar da rayuwar ƙasa.”
Hakazalika, Bio ya ce zai yi jagoranci ECOWAS cikin gaskiya da fifita buƙatun al’umma tare da inganta haɗin kan yankin.