Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kai ziyara Jihar Benuwe domin jajanta wa mutanen jihar bisa hare-haren da suka faru a wasu ƙauyuka kwanan nan.
Ya je ne domin nuna alhininsa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattaunawa da shugabanni don nemo mafita mai ɗorewa.
- Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato
- Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi
A yayin ziyarar tasa ta yini guda, Shugaba Tinubu ya fara ne da ziyartar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwe, inda ta duba waɗanda suka jikkata.
Shugaban ya shirya ganawa da iyalan waɗanda aka kashe, da waɗanda suka rasa muhallansu, da kuma shugabannin al’umma.
Hakazalika, Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki s jihar, ciki har da sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, shugabannin addinai, da ƙungiyoyin matasa.
Burinsa shi ne samo hanyar kawo ƙarshen rikicin da ya addabi yankunan Yelwata, Apa, da kuma Agatu.
Yadda rikicin ya samo asali
Rikicin a Jihar Benuwe ya daɗe ana tafka shi, kuma mafi yawan lokuta rikici ne tsakanin manoma da makiyaya.
Manoma na zargin cewa shanun makiyaya na lalata gonakinsu, yayin da makiyaya ke kukan rashin wuraren kiwo.
A watan Afrilun shekarar 2023, sama da mutum 50 ne suka rasa rayukansu a ƙauyen Umogidi da ke Ƙaramar Hukumar Otukpo.
A watan Yunin 2023 kuma, an kai farmaki ƙauyuka da dama a Guma da Logo, inda mutane da dama suka mutu.
An daɗe ana zargin wasu daga cikin hare-haren ƙungiyar Miyetti Allah da wasu ’yan bindiga ne ke kai wa.
Yawancin mutane sun rasa gidajensu da gonakinsu, wasu kuma sun tsere zuwa sansanonin ’yan gudun hijira.
Duk da irin ƙoƙarin da gwamnonin da suka gabata suka yi, har yanzu matsalar na ci gaba da faruwa.
Ziyarar Shugaba Tinubu tana ƙarfafa wa mutane gwiwa cewa za a iya samo mafita domin kawo ƙarshen kashe-kashen da ke faruwa a Benuwe da sauran wuraren da rikicin ya shafa.