✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu

Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su don su zama doka…

Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja.

A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar kudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka.

Kudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a fadin kasa, kafin daga bisani majalisun na wakilai da dattawa su amince da su.

Sanata Yemi ya ce, “Eh, yanzu kudurin ya bar hannunmu, yana kan hanyarsa ta zuwa wajen Shugaban Kasa domin ya sanya masa hannu ya zama doka.

“Kudurorin haraji irin wadannan suna bukatar taja da tsifa sosai. Dole bangarorin masana shari’a na zaurukan majalisun biyu su tabbatar kudurorin sun yi daidai da dokokin da ake da su a kasa kafin su tura wa Shugaban Kasa.

“Ba aiki ba ne na kwana biyu ko uku. Bayan an kammala aikin daidaita su kuma Akwun Majalisar Dokoki ta Kasa zai mayar da su kundi daya. Bayan haka ne kawai Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su sa hannu a aike da su,” in ji Sanatan.