Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana shirin kafa dokar da za ta mayar da rantsar da shugaban kasar a kwaryar majalisar, maimakon yadda ake yi a dandalin taro na Eagle da ke tsakiyar birnin Abuja.
DW ta ruwaito cewa ita dai Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 ta yi fice wajen dauko batutuwan da ke haifar da cece-kuce, kama daga yunkurin mayar da yin zabe ya zama dole da kuma hukunta duk wanda ya ci mutuncin taken Nijeriya sai kuma wannan batu na amfani da doka domin sauya tarihin da aka daura dambarsa tun a shekara ta 1999 da aka sake kafa dimokuradiyya a kasar.
- Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya
- Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC
Tun daga wannan lokaci kawo yanzu ana rantasar da shugaban kasar ne a dandalin taro na kasa na Eagle da ke birnin Abuja, wurin da ke bayar da dama ga dubban ’yan Nijeriya su cire kwarkwatar idanuwansu yayin rantsar da shugaban da suka zaba.
A yanzu Majalisar Dattawan na son canza wannan al’ada, har ma da gwama batun da sanya shugaban Nijeriya ya rinka jawabi ga ‘yan majalsar a duk ranar dimukurdiyya 12 ga watan Yuni.
Tuni wannan mataki ya janyo mayar da martani a Nijeriyar, musamman wadanda da su aka yi gwagwarmayar yanke cibiyar sake kafa dimokuradiyya a kasar.
Domin sauya batu na tarihi ga muhimmin al’amari muhimmi ne a Nijeriyar, musamman danganta shi da ranar 12 ga watan Yuni da aka soke zaben da ake dangata shi da mafi sahihanci.
Sabo dai akan ce tirken wawa, domin shekaru 26 kenan da sake kafa dimokuradiyya da ake rantsar da sabon shugaban Nijeriya a dandalin Eagle din da ke tsakiyar birnin duk bayan shekaru hudu.
Majalisar Dokokin Nijeriyar dai kan gwada ta ga martanin ’yan kasar a kan wasu al’amura, inda daga baya ta kan janye batun wanda shi ne damar da dimukurdiyya ta bai wa ’yan kasa.