Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya nesanta kansa daga wata kungiya da take fafutukar ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a 2027.
Mai magana da yawun Sanatan, Isma’il Mudashir ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce a maimakon haka, kamata ya yi kungiyar ta fi mayar da hankali wajen mara wa Tinubu baya ya samu nasarar yunkurinsa na bunkasa Najeriya.
A kwanan nan ne dai wata kungiya mai suna Zauren Matasan APC na Arewacin Najeriya (NNPYA) ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu ya dauki Sanatan a matsayin wanda za su yi takara tare.
- Gwamnatin Nijeriya ta yi wa Amurka martani kan barazanar tsaro a Abuja
- Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha
Hakan dai ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ’yan kwanakin nan cewa ba lallai ne Tinubun ya sake yin takara tare da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a 2027 din ba.
A cewar Sanata Barau, “An jawo hankalina kan wasu rubuc-rubuce a shafukan sada zumunta da ma wasu jaridu na wasu kungiyoyi, cikinsu har da NNPYA, inda suke kiran jagoranmu, Shugaba Bola Tinubu, da ya dauke ni a matsayin mataimaki a 2027. Wannan ba da yawuna ba ne kuma ba shi ne abu mafi muhimmanci ba a yanzu.
“Ina kira ga NNPYA da ma sauran kungiyoyin da ke wannan fafutukar da su daina daga yanzu, sannan su mayar da hankalinsu wajen goyon bayan yunkurin Shugaba Tinubu na magance matsalolin da ke addabar kasarmu.
“Kamata ya yi mu hada karfi da karfe wajen goyon bayan Tinubu har ya samu ya kai Najeriya tudun mun tsira.
“Yanzu ba lokaci ne da za mu rika wannan kiraye-kirayen ba, lokaci ne na tabbatar da cewa Tinubu ya samu nasarar sauke nauyin da ke wuyansa.
“Ya damu kwarai da gaske wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba. Saboda haka nake kira da kowa ya goya masa baya kan kudurorinsa da tuni aka fara ganin amfaninsu a kasa,” in ji Sanata Barau.