Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta sami dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natsha Akpoti-Uduaghan da laifin raina kotu, sanna ta ci ta tarar naira miliyan biyar.
Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta ce Natasha ta wallafa wata wasikar zambo ta ban hakuri ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, duk da umarnin kotun na baya.
- ’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike
- Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC
A cewar kotun, wasikar zambon, wacce Natasha ta wallafa a shafinta na Facebook ranar bakwai ga watan Afrilu, rain ice ga umarnin da kotun ta bayar a baya ga dukkan bangarorin guda biyu.
A kan haka ne kotun ta ba Natasha wa’adin mako daya ta wallafa sakon ban hakuri a shafukan manyan jaridu guda biyu da kuma a shafin nata na Facebook.
Bugu da kari, kotun ta uamrce ta da ta biya tarar naira miliyan biyar saboda aikata laifin.
Kodayake dai hukuncin na kotun nay au ya biyo bayan bukatar hakan da Akpabio ya yi, amma kotun ta ki amincewa da dukkan ragowar bukatun nasa.