✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa

Mai Shari'a Binta Nyako ta ce hukuncin da majalisar ta ɗauka a kan Sanata Natasha ya yi tsauri da yawa.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci Majalisar Dattawa da ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

A watan Maris, Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.

Taƙaddamar ta samo asali ne kan yadda aka canja tsarin zama a zauren majalisar.

Bayan dakatarwar, Natasha ta zargi Akpabio da yunƙurin cin zarafinta, inda ta kai ƙara Majalisar Ɗinkin Duniya kan lamarin.

A ranar Juma’a, Mai shari’a Binta Nyako ta yanke hukunci cewa dakatarwar watanni shida da aka yi wa Natasha ta yi tsanani.

Ta ce dokar da Majalisar Dattawa ta dogara da ita ba ta fayyace adadin kwanakin da za a iya dakatar da ɗan majalisa ba.

Alƙalin kotun ta ƙara da cewa, tun da ‘yan majalisa ke da kwanaki 181 kacal da suke zama a kowane zangon mulki, dakatar da ɗan majalisa tsawon wannan lokaci na nufin mutane daga yankinsa ba za su samu wakilci ba.

Mai shari’a Nyako ta ce ko da yake Majalisar Dattawa na da ikon hukunta mambobinta, amma hakan bai kamata ya kai ha hana al’umma samun wakilcinsu ba.

Don haka kotun ta umarci Majalisar Dattawa ta mayar da Natasha bakin aikinta.