Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce rashin samun wurin da jirginsa zai sauka ne a filin jirgin sama na Katsina ya sa bai samu halartar jana’izar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.
A ranar Talata ce dai aka binne Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina bayan rasuwarsa a asibiti a Landan ranar Lahadi, yana da shekara 82.
- Buhari: Ƙasar China ta yi rashin babban aboki – Xi Jinping
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Najeriya Ba Sa Samun Adalci
To sai dai Akpabio ya ce duk ƙoƙarin direban jirginsu na samin wurin yin fakin ya ci tura, tilas suka koma Abuja.
A wani saƙo da Akpabio ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba, ya ce, “Jiya, direban jirginmu ya yi ta ƙoƙarin sauka a filin jiragin sama na Katsina, amma saboda cunkoson jirage da rashin wurin fakin, dole muka hakura muka koma Abuja. Abin da ya hana a gan ni a wajen jana’izar Buhari ke nan.
“Amma yau [Laraba], na sami rakiyar abokaina Sanatoci inda muka ziyarci iyalan Buhari a gidansa na Daura, muka yi musu ta’aziyya.
“Mun kuma yi masa addu’ar neman gafarar Allah sannan mun jajanta wa matarsa da ’ya’yansa da sauran ’yan uwansa,” in ji Akpabio.
Shugaban majalisar ya kuma ce daga nan sun ziyarci Sarki Daura, Alhaji Umar Farouk Umar domin ya masa ta’aziyya.
Ya ce sun kuma ce sun ziyarci Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, inda shi ma suka yi masa ta’aziyyar.