✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari: Ƙasar China ta yi rashin babban aboki – Xi Jinping

Shugaban Ƙasar China, Ci Jinping, ya miƙa sakon ta’ziyyarsa ga Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, bisa rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban Ƙasar China, Ci Jinping, ya miƙa sakon ta’ziyyarsa ga Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, bisa rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin sakon ta’aziyyarsa ranar Laraba a madadin gwamnati da al’ummar China, Xi ya ce suna taya gwamnatin Najeriya da iyalan tsohon shugaban alhinin rasuwarsa.

Ya bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba da ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban ƙasa da haɗin kanta, kuma ana girmama shi a faɗin duniya.

Shugaban na China ya ce zamanin mulkin Buhari, ya kyautata ƙawance da kasarsa da ma alaƙarta da sauran ƙasashen Afirka, inda ya ce rashinsa ya sa ƙasarsa ta yi rashin babban aboki.

Xi Jinping ya kuma ce China na mutunta alaƙarta da Najeriya kuma a shirye take ta ci gaba da ganin kyakkyawar alaƙar ta ci gaba da wanzuwa.