✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gawar Buhari ta kama hanyar Daura daga Katsina

Manyan sojoji ne suka saukar da gawarsa, wadda aka lullube da tutuar Najeriya, daga Jirgin Fadar Shugaban Kasa a Filin Jirgin Sama na Katsina

A kama hanyar zuwa Daura, mahaifar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gawarsa domin yi mata sallah da kuma binne shi.

An tafi da gawar ce a cikin motar daukar marasa lafiya ta soji, jim kadan bayan an kawo ta daga birnin Landan na kasar Birtaniya, inda Allah Ya yi wa Buhari rasuwa a asibiti a ranar Lahadi, yana da shekara 82 a duniya.

Manyan sojoji ne suka saukar da gawarsa, wadda aka lullube da tutuar Najeriya, daga Jirgin Fadar Shugaban Kasa a Filin Jirgin Sama na Katsina, a matsayinsa na tsohon Janar din soji, inda ya samu tarba irin ta soji.

Gawar ta iso Katsina ce da rakiyar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da ’yan tawagarsa da Shugaban Kasa Tinubu ya tura domin dauko ta, da kuma iyalan marigayin.

Shugaba Tinubu da Shettima, da Manyan sojoji da sauran jami’an tsaro da Gwamnan Jihar Katsina, Umaru Dikko Radda, da wakilai daga kasashen waje ne suka karbi gawar, tare da yi mata rakiya aka sanya domin wucewa da ita Daura.

Gawar Buhari a cikin mota da rakiyar sojoji a yayin da za a kai ta Daura

Tuni Tinubu ya hau helikwafta zuwa Daura inda attairai da sarakuna da gwamnoni da ministoci da manyan jami’an gwamnati — tsofaffi da masu ci — daga ciki da wajen Najeriya suke ta tururuwa domin halartar jana’iza da kuma mika ta’aziyya.

A safiyar Talatar nan suka baro London, kuma za za a gudanar da jana’iza sa’annan a binne Buhari ga gidansa da ke Daura.

Buhari shi ne zababben shugaban kasan Najeriya na biyu dan asalin Jihar Katsina, bayan Umaru Musa ‘Yar Adua, wanda ya rasu a kan karagar mulki.
Bayan rasuwar Umar, mataimakinsa, Goodluck Jonathan ya ci gaba da mulki, sa’annan ya kara wa’adi daya.

A shekarar 2015 kuma Buhari, wani dan asalin Jihar Katsina ya kayar da Jonathan, inda ya zama shugaban kasar Najeriya na 15.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin zababben shugaban kasa, inda ya mika jagorancin kasar ga Shugaban Kasa mai ci, Bola, Ahmed Tinubu.