A Talatar nan za a yi jana’izar tsohon shugaban ƙasa Marigayi Janar Muhammadu Buhari a mahaifiyar da ke Daura a Jihar Katsina.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kansa zai ƙarbi gawar Buhari da Azahar kuma tuni ya kafa kwamitin manyan jami’an gwamnati domin gudanar da tsare-tsaren jana’izar.
Tun a ranar Lahadi da Buhari ya rasu, Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashin Shettima, ya je ya kula da tsare-tsare da kuma rako gawar daga ƙasar Birtaniya inda Allah Ya yi wa tsohon Shugaban rasuwa, zuwa Najeriya.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a garin Daura, inda manyan baƙi daga sassa daban-daban ke ta tururuwar zuwa domin halartar jana’izar Buhari wanda ya rasu bayan jinya yana da shekara shekara 82.
- Tare aka kwantar da ni da Buhari a asibitin da ya rasu —Janar Abdussalami
- NAJERIYA A YAU: Wa Zai Gaji Buhari A Fagen Siyasar Najeriya?
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talatar nan a matsayin ranar hutu domin Jana’izar Buhari, wanda shi ne ya miƙa mulki ga Shugaba Tinubu.
Aminiya ta samu bayani cewa bayan isowar gawar Buhari za a yi mata Sallar Jana’iza a garin Daura da Azahar, sa’annan a binne ta a gidansa da ke garin.
Wakilinmu a garin Daura ya lura am tsaurara tsaro a ƙofar shiga Masarautar Daura da kuma gidan Buhari da ke unguwar GRA a kan hanyar zuwa Kongolam.
Hakazalika an tsaurara tsaro a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina; baya ga shingayen bincike guda 12 da jami’an tsaro suka kafa daga Katsina zuwa garin Daura.
Buhari wanda ya mulki Najeriya sau biyu a matsayin shugaban mulkin soja da kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti a birnin Landan da ke ƙasar Birtaniya.
Manya na tururuwar zuwa ta’aziyya Buhari
Manyan mutane da suka ziyarci gidan Marigayin domin yin ta’aziyya sun haɗa da tsofaffin gwamnoni da ministoci da jami’an tsohuwar gwamnatin Buhari kamar tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun.
Sauran sun haɗa da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami; tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da kuma Ministan Gidaje, Ahmed Musa Dangiwa.
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari da tsohon kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan da sauransu na daga cikin masu ziyarar.
Dun da cewa yawancin manyan baƙin sun koma Kastina ko Kano domin kwana, wakilimmu ya lura cewa an riga an kame ɗakuna a kusan ɗauƙacin otel-otel da masaukan baƙin da ke garin Daura.
Jami’an Gwamnati sun yi wa Daura tsinke
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ziyarci garin na Daura domin garin yadda shirye-shiryen jana’izar ke gudanar, ind ya yi rangadi da kuma kula da zirga-zirgar ababen hawa.
Gwamnan ya kuma ziyarci Fadar Sarkin Daura, Dakta Umar Farouk Umar, inda ya miƙa ta’aziyya, inda limamai suka yi wa Buhari addu’o’in samun rahama.
Da safiyar ranar Litinin, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruk Joɓe, da Mataimakin Shugaban Ma’aikatansa, Mukhtar Saulawa; da Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Katsina, Sani Daura; da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Nasiru Muazu Danmusa; da tsohon Shugaban Hukumar Ilmi Bai-ɗaya ta Jihar Katsina, Lawal Daura da Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda mai kula da Shirya ta 14, Aliyu Musa, sun ziyarci garin na Daura.