✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa marigayi Buhari salatul ga’ib a Jos

Mu duka mutane ne, muna da kasawarmu. Buhari yana da nasa kurakuran, don haka muna rokon Allah Ya jikansa da rahama.

Wasu mazauna garin Jos, babban birnin Jihar Filato, sun gudanar da sallar jana’iza ta salatul ga’ib ga marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

An gudanar da sallar janaizar ce a yammacin ranar Litinin din nan a Unguwar Yandoya da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a jihar ta Filato.

A jiya Lahadi ce dai tsohon shugaban kasar ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti da ke birnin Landan, wanda za a yi jana’izarsa ranar Talata, a mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina.

Sai dai gabanin haka wasu mazauna garin Jos suka gabatar da sallar jana’iza ta ga’ib wadda ta sami halartar gomman mutane da suka fito daga unguwanni daban-daban, na garin na Jos.

A cewar mazauna garin, halartar sallar da suka yi, ita ce hanyar da za su bi domin yi wa marigayin addu’a da roko masa Rahamar Allah.

Da yake jawabi, Malam Muhammad Buhari, wanda ya jagoranci jana’izar, ya ce marigayin wanda a lokacin da yake shugabancin Nijeriya, ya bayar da gudunmawa sosai duk da cewa yana da nasa kura-kurai da ya yi, amma ya cancanci a karrama shi.

Limamin ya kara da cewa sanarwar da matar mamacin A’isha Buhari ta yi wa ‘yan Nijeriya, a madadin mijinta na nema masa yafiyar kura-kuran da ya yi, shi ya sanya suka shirya addu’ar.

Ya ce sallah da kuma addu’ar da suka yi ta yi daidai da koyarwar addinin Musulunci, domin an yi irin wadannan addu’o’i a zamanin Annabi Muhammad SAW.

Wani shugaban al’umma, Garba Daho Muhammad Sagir Umar, wanda ya halarci jana’izar, ya bayyana cewa Shugaba Buhari, ya cancanci a yi masa addu’a bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa.

“Tunda ba za mu iya zuwa Katsina don halartar Sallar Jana’izar ba, sai muka ga ya dace mu yi sallarmu daga Jos, kuma mu roki Allah Ya gafarta wa tsohon Shugaban Kasa Buhari.

Shi ma Abdullahi Sulaiman, wanda ya halarci sallar jana’izar ya ce, “Da na so in kasance a Katsina, domin halartar jana’izar amma ba ni da karfin yin hakan.

“Amma saboda in nuna girmamawata ga tsohon shugaban kasa, na halarci wannan addu’ar a Jos, ina rokon Allah Ya gafarta masa. Mu duka mutane ne, muna da kasawarmu. Buhari yana da nasa kurakuran, don haka muna rokon Allah Ya jikansa da rahama”.