Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Katsina, wanda za a yi wa jana’iza a Daura.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da hakan da yammacin yau Litinin a Abuja.
- HOTUNA: Tinubu ya kafa kwamitin jana’izar Buhari
- HOTUNA: Kashim Shettima ya yi wa iyalan Buhari ta’aziyya a Landan
A cewar ministan, da misalin karfi 12 ranar gobe Talata ake saran gawar marigayi tsohon shugaban za ta isa Katsina.
Sannan za a yi wa shugaban faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina, kafin daga bisani a wuce garin Daura da gawarsa.
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima yanzu haka na Landan, kuma shi ne zai rako gawar har Katsina.
Tuni dai Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamiti na musamman da zai tsara jana’izar da kuma duk wani abu da ake bukata wajen binne shugaban.