Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya yi wa wasu daga cikin iyalan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta’aziyya a birnin Landan.
Kashim Shettima ya isar da gaisuwar ne ga mai ɗakin mamacin Aisha Buhari da kuma ɗan uwansa Mamman Daura.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya samu rakiyar Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila.
Sauran jami’an gwamnatin da ke Landan domin rasuwar tsohon shugaban ƙasar sun haɗa da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar da Gwamnan Borno Babagana Zulum.
A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban ƙasar ya isa birnin Landan domin rako gawar marigayi shugaba Buhari zuwa Nijeriya kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya umarce shi.
A ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan bayan fama da jinya.