✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba da hutu a Nijeriya saboda rasuwar Buhari

An ayyana hutu gobe Talata a dalilin rasuwar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Talata a matsayin ranar hutu saboda ’yan ƙasa su yi jimamin rasuwar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Mista Olubunmi Tunji-Ojo ya ce an ba da hutun ne bayan samun sahalewar Shugaba Bola Tinubu kan hakan.

Sanarwar da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan, Dokta Magdalene Ajani ta fitar, ta ce an ayyana hutun ne domin nuna irin girmamawa da kuma tuna gudunmawar da marigayi Buhari ya bayar a fannin dimokuradiyya da ci gaban ƙasa.

“Gwamnatin Nijeriya tana godiya ga hidima da sadaukarwar da ya yi domin ciyar da ƙasar gaba.

“Muhammadu Buhari ya mulki Nijeriya da gaskiya da amana da kuma matuƙar sadaukarwa musamman wajen haɗin kan ƙasar da ci gabanta.

Kazalika, sanarwar ta ambato Ministan yana kira ga ’yan Nijeriya da su tuna mamacin ta hanyar koyi da shi wajen ɗabbaƙa zaman lafiya da son ci gaban ƙasar da aka san marigayin da su.

A yayin da Gwamnatin Tarayyar ke ci gaba da yi wa mamacin addu’a, ta sake miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Jihar Katsina da kuma ɗaukacin ’yan ƙasa dangane da wannan babban rashi.

Tuni dai Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yammacin Nijeriya ta bayyana kaɗuwarta kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 a birnin Landan.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wanda shugabanta, Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda ya fitar, ya ce Buhari tamkar uba yake a gare su.

“Muna miƙa ta’aziyarmu ga Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da iyalai da ’yan uwa da mutanen Jihar Katsina da ma ’yan Nijeriya baki ɗaya bisa wannan babban rashin da aka yi.”

Gwamnonin sun ce Buhari abin alfaharin yankinsu ne, “wanda ya ƙarar da rasyuwarsa wajen hidima da sadaukar da kansa wajen ciyar da Najeriya gaba.

“Saboda wannan ne ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma suka amince da ayyana ranar Talata, 5 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar hutu domin jimamin rasuwar mamacin,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Dikko Radda ya ce gawar Buhari za ta isa Katsina a gobe Talata da misalin ƙarfe 12, sannan a gudanar da jana’izar da misalin ƙarfe biyu na rana.

“Muna kira ga dukkan ’yan Nijeriya su yi masa addu’a. Allah ya jiƙansa, sannan muna addu’ar Allah ya ba iyalana da ma dukkan ’yan ƙasar juriyar rashinsa.”