✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare aka kwantar da ni da Buhari a asibitin da ya rasu —Janar Abdussalami

“Da rasuwar Buhari, tabbas siyasar Najeriya za ta canza — ina fatan za ta yi kyau,” in ji Janar Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa a asibiti ɗaya aka kwantar da shi da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda Allah Ya yi wa Buharin rasuwarsa a ƙasar Birtaniya.

A wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, Abdulsalami ya bayyana cewa an sallame shi ne daga asibitin jim kadan kafin ya samu labarin rasuwar Buhari.

Ya ce, “A asibiti daya aka kwantar da mi, amma abin takaici bayan an sallame ni na samu labarin rasuwar.”

Ya ci gaba da cewa, “Don haka, lokacin da na ji labarin rasuwarsa, nan take na garzaya wurin don ta’aziyyar iyalansa da kuma ganin abin da za a iya yi don shirya gawar domin a dawo da ita Najeriya.”

Yayin da yake waiwaye kan dangantakarsu ta shekaru da dama, Abdulsalami ya bayyana cewa alakarsu da Buhari ta fara ne tun a shekarar 1962 lokacin da dukansu suka shiga aikin soja.

Abdulsalami ya tuna cewa, “Yana gaba da ni; kuma a lokacin yakin basasa, tare da shi muka yi faɗa a ɓangare daya da shi.”

Ya bayyana marigayi Buhari a matsayin “mutum mai kirki, mai shiru-shiru da kuma gaskiya da riƙon amana sosai.”

Abdulsalami ya kara da cewa, “Za ka iya amincewa da Buhari da komai a duniya kuma ba zai ci amanarka ba.”

Game da mulkin Buhari, Abdulsalami ya yaba da matsayinsa na yaki da cin hanci da rashawa, amma ya amince da gazawar wasu jami’an gwamnatinsa.

Ya bayyana cewa, “Lokacin da ya zama shugaban kasa na dimokuraɗiyya, ya yi iyakar ƙoƙarinsa a wajen yaƙi da cin hanci da rashawa. Abin takaici, an samu wasu jami’an gwamnatin da laifi. Ba su yi abin da ake tsammani daga gare su ba.”

Abdulsalami ya kira mutuwar Buhari “babban rashi” ga Najeriya da kuma yankin kudu da Sahara.

Ya bayyana cewa shawarar da Shugaba Tinubu ya yanke na tura Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Shugaban Ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, zuwa Birtaniya domin kula da dawo da gawar Buhari “ya nuna girman abin da ya samu Najeriya.”

Tsohon shugaban kasar ya kammala da cewa, “da rasuwar Buhari, tabbas siyasar Najeriya za ta canza — ina fatan za ta yi kyau.”