✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naira: Kotu ta yanke wa Hamisu Breaker da G-Fresh hukunci ɗaurin wata 5

Kotun ta ci tarar kowane daga cikinsu kuɗi Naira 200,000.

Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta yanke wa fitaccen ɗan Tiktok, Al-Ameen G-Fresh da mawaƙi Hamisu Breaker, hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan yari bayan samun su da laifin wulaƙanta takardun Naira.

Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukunci, inda ya yi musu ɗaurin wata biyar a gidan yari, bayan sun amsa laifin da ake tuhumarsu a gaban kotu.

Hukuncin ya biyo bayan tuhumar da Hukumar EFCC ta shigar da su a gaban kotu, bisa laifin wulaƙanta Naira.

A cewar ƙarar, G-Fresh ya watsa kuma ya taka takardun Naira 1,000 har na Naira 14,000 yayin da yake rawa a shagon wata mai suna Rahma Sa’idu a Ƙaramar Hukumar Tarauni.

Shi kuma Hamisu Breaker, ya watsa Naira 30,000 na takardun Naira 200 a wani taron walima da aka yi a Hadeja da ke Jihar Jigawa.

Dukkaninsu sun aikata laifin ne a watan Nuwamban 2024.

Laifin ya ci karo da Sashe na 21(1) na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007, wadda ta haramta cin zarafi ko wulaƙanta Naira.

Bayan amsa laifinsu, kotun ta ba su damar biyan tara maimakon zaman gidan yari.

Kowannensu ya biya tarar Naira 200,000, wanda hakan ya sa aka sake su bayan tsare su.

Wannan hukunci na nuna cewa gwamnati na ɗaukar wulaƙanta Naira a matsayin babban laifi, duk da cewar akwai damar samun beli ko biyan tara.