Shugaban Hukumar Yaƙi Da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce hukumar na binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki a yanzu haka.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Legas, yayin wani taron wayar da kai kan illar wulaƙanta takardun Naira.
- AGILE: ’Yan mata 40,630 za su samu tallafin karatu a Yobe
- ICPC ta gurfanar da ma’aikatan gwamnati kan karkatar da kudaden Bankin Duniya
Olukoyede, ya ce EFCC ba za ta jira har sai gwamnonin sun sauka daga mulki kafin a fara bincikensu ba.
Amma ya ce za su ɗauki mataki a kansu ne bayan sun gama wa’adin mulkinsu.
Ya kuma bayar da labarin wani tsohon gwamna da ya tsere zuwa Ingila kwana guda bayan ya sauka daga mulki, domin guje wa shiga hannun EFCC.
A cikin makon, tsohon gwamnan ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa a wani otel.
A lokacin bikin, ya yi liƙi da kuɗin Ingila, abin da ya bai wa ma’aikatan otel ɗin mamaki.
Manajan otel ɗin ya zaci yana da matsala, ya kira ‘yan sanda.
Bayan ’yan sanda sun isa, har suna shirin saka shi a motar asibiti saboda sun ɗauka cewa yana da taɓin hankali.
Amma abokansa da wasu gwamnoni biyu daga Najeriya, suka bayyana cewa ba shi da wata matsala, kawai tsohon gwamna ne da ke murnar ranar haihuwarsa.
Olukoyede, ya kawo wannan labari ne don nuna irin halin da wasu ’yan siyasa ke yi bayan sun sauka daga mulki, da kuma jaddada cewa EFCC za ta ci gaba da yaƙi da cin hanci da rashawa.