✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan kasuwar Kano ya yi barazanar maka EFCC a kotu kan zargin ɓata masa suna

EFCC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan gaza samun ɗan kasuwan.

Wani ɗan kasuwa a Jihar Kano, Rabiu Auwalu Tijjani, ya ce zai maka Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a kotu, bisa zargin ɓata masa suna, bayan ta ayyana shi a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo.

EFCC, ta zargi Tijjani da zamba da kuma almundahanar kuɗi da suka kai dala miliyan 1.9.

Amma Tijjani, ya ce hulɗar kasuwanci ta gaskiya ya gudanar tsakaninsa da wani mutum mai suna Ifeanyi Ezeokolu da kamfanoninsa, inda suka yi musayar kuɗi har dala miliyan 77 daga watan Janairu zuwa Disamban 2023.

Yayin da yake magana daga birnin Dubai, inda yake zaune, Tijjani, ya ce matakin da EFCC ta ɗauka ya ba shi mamaki.

Ya ƙara da cewa, shi ne aka cuta a kasuwancin, amma yanzu ana ƙoƙarin nuna shi a matsayin ɗan damfara.

Ya bayyana cewa Ifeanyi na turo masa Naira, sannan shi kuma ya mayar masa da kuɗin zuwa dala.

Ya ce wannan kasuwanci ya wakana sau da dama, tare da kamfanoni 11 da Ifeanyi ke da su.

Daga baya, Tijjani ya gano cewa Ifeanyi ya karɓi sama da adadin da ya kamata a ba shi.

Yayin da ya nemi su gyara matsalar, Ifeanyi ya fara tsaiko a lamarin.

Tijjani ya kai wa Hukumar DSS ƙorafi, inda ta bayar da shawarar ɗauko ƙwararren mai bincike don tantance bayanan asusun bankinsu.

Tijjani, ya ce maimakon su bi hanyoyin sulhu, sai Ifeanyi ya kai DSS ƙara kotu, inda ya ce an tauye masa haƙƙi.

Yanzu haka, lamarin yana gaban kotu, kuma Tijjani, ya ce ya tura wakili zuwa EFCC domin ya wakilce shi.

Mai binciken da Tijjani ya ɗauka, Mista Olumide Ajayi, ya ce sun gano cewa kamfanonin Ifeanyi sun karɓi sama da abind a ya kamata a ba su da kusan dala miliyan biyu.

Ya ƙara da cewa Ifeanyi ya gabatar da bayanan asusun kamfanoni 9 kacal daga cikin 11 da suka yi hada-hadar kasuwancin.

Ya ce har yanzu Ifeanyi bai kawo bayanan asusun kamfanonin GRE International Company for Trading and Supplies da kuma Seagate Maritime Limited, waɗanda aka yi cinikayyar da ta haura dala miliyan 50.

Da aka nemi jin ta bakinsa, Ifeanyi ya ƙi cewa uffan kan lamarin, sai dak ya ce lamarin na gaban EFCC.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce sun ayyana Tijjani a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo ne bayan sun gaza samun shi ta kowace hanya.