Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta wa Tarayyar Turai da kuma Mexico harajin kashi 30 kan kayayyakin da ake shiga da su da su ƙasar daga ranar 1 ga Agusta.
Bayanai sun ce ana ganin wannan matakin zai iya haddasa rikici mai tsanani tsakanin Amurka da biyu daga cikin manyan abokan kasuwancinta.
- An sanya dokar hana fita a Adamawa
- Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil
Trump ya yi cikakken bayani kan wadannan haraje-harejen ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa matuƙar ba a cimma wata tartibiyar matsaya ba, ba shakka zai ƙara lafta musu harajin.
Wannan na daga cikin jerin sabbin haraje-haraje da Trump ke kara wa abokan kasuwancin Amurka a wani abu da ya zama ginshiki yayin yakin neman zabensa.
Mista Trump ya ce matakin zai zama tushen farfado da tattalin arzikin Amurka, inda ya zargi sauran kasashe da zaluntar Amurka na tsawon shekaru.
A cikin wasikarsa ga shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, Trump ya yarda cewa kasar ta taimaka wajen dakile kwararar bakin haure da miyagun kwayoyi irin su fentanyl zuwa Amurka.
Amma ya ce Mexico ba ta yi isasshen kokari ba don hana Arewacin Amurka zama dandalin masu safarar miyagun kwayoyi.
A cikin wasikarsa zuwa ga Tarayyar Turai kuma, Trump ya bayyana cewa gibin cinikayya tsakanin Amurka da EU barazana ce ga tsaron kasa.
A martaninta ga wannan matakin, Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta fada a ranar Asabar cewa EU na shirye ta dauki matakin rama wa kura aniyarta don kare muradun tarayyar idan Amurka ta sanya harajin kashi 30 cikin 100 kan kayayyakin Turai daga ranar 1 ga Agusta.
Sai dai von der Leyen wacce ke kula da kasuwancin kasashen EU 27 ta ce kungiyar tana da niyyar ci gaba da kokarin cimma yarjejeniya kafin sabon wa’adin na shugaba Trump.
Ta kara da cewa kasashen kalilan ne ke yin dalla-dalla kan harkokin cinikayya kamar Tarayyar Turai tare kuma da bin ka’idojin kasuwanci na gaskiya.
Shugabar ta EU ta yi kalaman ne a matsayin martani kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya sake yi a ranar Asabar, wacce ke kara tayar da fargabar barkewar yakin kasuwanci da Turai ke fatan kauce wa.
Von der Leyen ta kuma ce EU za ta dauki duk matakan da suka dace don kare muradunta ciki har da ramawa kura aniyarta idan bukatar hakan ta taso.