✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka

Musk ya ce zai kafa jam'iyyar da za ta goyayya da jam'iyyu biyu da Amurka ke da su.

Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka.

Musk, wanda attajirin mai kuɗi sosai, ya ce jam’iyyarsa za ta kasance wata hanya ta daban daga jam’iyyu biyu da ake da su yanzu, wato Republican da Democrat.

Amma har yanzu ba a bayyana ko hukumar zaɓen Amurka ta amince da rajistar jam’iyyar ba.

Amma Musk bai bayyana wanda zai jagoranci jam’iyyar ko irin manufofinta ba.

Tun da farko Musk ya fara maganar kafa sabuwar jam’iyya ne bayan samun saɓani da Donald Trump, wanda hakan ya kai sa ga sauka daga matsayinsa a gwamnatin Trump.

Yayin wata ƙuri’ar jin ra’ayi da ya gudanar a X, mutane miliyan ɗaya ne suka kaɗa ƙuri’a, kuma kashi 60 daga cikinsu sun amince a kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka.