✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta dakatar da bai wa Ukraine tallafin makamai

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya shawarci Ukraine din da ta mika wuya.

Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su.

Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta dakatar da duk wani tallafin makamai da take bai wa Ukraine din.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada hare-harenta a kan kasar, yayin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza yaki tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna.

Rahotanni na cewa, Ukraine za ta shiga tsaka mai wuya, musamman yadda za ta ci gaba da fuskantar Rasha ba tare da irin makaman Amurka ba,  yayin da Shugaba Vladimir Putin, ya shawarci Ukraine din da ta mika wuya.

Tuni aka shiga damuwa a wannan kasa da ke gabashin Turai, inda gwamnatin kasar ke ganin daga lokacin da aka fara samun tsaikon tallafin Amurka, Rasha za ta kara samun kwarin gwiwar kai farmaki babu kakkautawa.

A halin da ake ciki Ukraine ta shiga tsaka mai wuya, domin baya ga katse tallafin makamai, matakin da shugaba Trump ya dauka na dakatar da ayyukan Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka, ya shafi ayyukan jin kai a wannan kasa, sakamakon cewa tana cikin kasashen da suke karbar tallafin USAID sosai.