Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta.
An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata.
- Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027
- Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji
Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa tiyata.
Tun bayan fara shirin a shekarun baya, sama da mutum 3,000 ne suka ci gajiyar aikin tiyatar da aka gudanar a wurare daban-daban.
A wannan karon, Mangal ya bayar da Naira miliyan 20 daga cikin tallafin domin yi wa mutum 100 tiyata a kan cutar mafitsara da kuma lalurar gwaiwa.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Adamu Aliyu, ya ce da babu wannan tallafi, da har yanzu yana fama da cutar saboda ba shi da isasshen kuɗi don biyan kuɗin tiyatar.
Alhaji Mangal ya fara bayar da irin wannan taimako tun shekarar 2016, kuma tallafin yana zuwa har wasu maƙwabtan jihohi da ma Jamhuriyar Nijar.
Wata mata da ta nemi a sakaya sunanta ta ce wannan aiki ya zama darasi ga masu hali da ba sa son taimakon jama’a.
“Tun sama da shekara 20 Alhaji Mangal ke ciyar da marasa ƙarfi da abinci, kuma har yanzu bai fasa ba,” in ji ta.