Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayayyakin noma ga magidanta 1,000 da suka hada da ‘yan gudun hijira daga Mandunari da ke karamar hukumar Gujba da sauran al’ummomin da suke zaune a yankin.
Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Damaturu, Buni ya bayyana cewa, duk da cewa al’ummomin Mandunari ya kasance su ne yankin al’umma guda daya tilo a jihar Yobe da har yanzu ba a sake tsugunar da su ba, al’ummarta sun nuna jajircewarsu na komawa gidajen kakanninsu.
- Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump
- Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da dawowar duk ‘yan gudun hijira lafiya, tare da tallafa musu ta hanyar saka hannun jari a ayyukan more rayuwa, tsaro, gidaje, kiwon lafiya, da ilimi.
Kayayyakin da aka bada tallafi ga manoman sun hada da ingantattun kayayyakin yin noma da irin masara, kubewa, gyada, gero, da irin shinkafa, taki, maganin kashe kwari da na ciyawa da makamantansu.
“A lokacin rani, manoma za su sami famfunan ruwa da ingantattun irin albasa, tumatir, kabeji, latas, da barkono.
“Gwamnatin jihar Yobe ta riga ta zuba jarin sama da dala biliyan 4 a ayyukan noma a fadin al’ummomi 178 na mazabun Jihar, inda ta samar da taraktoci, takin zamani, da sauran kayan masarufi don bunkasa samar da abinci,” inji gwamnan.
Ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar hukumar raya kasa da hadin gwiwar kasar Switzerland za ta tallafa wa karin magidanta 2,000 da kayan noma da kiwo a Gaidam, Tarmuwa, da Damaturu.
Buni ya kara da cewa, kananan manoma za su kuma samu horo kan noma da kiwo da sauyin yanayi, yayin da a karkashin shirin samar da mafita mai dorewa manoma 1,000 da ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta horas da su za su samu kananan tallafi don ci gaba da rayuwarsu.
“Muna ci gaba da jajircewa wajen ganin ba a bar wata al’umma a baya ba, duk wanda ya rasa matsugunai ya cancanci a ba shi dama mai kyau don sake gina rayuwarsu cikin aminci da mutunci,” in ji gwamnan.