✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka

Baturen ’yan sandan yankin Kerr County, ya sanar da cewa masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane sama da 800

Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar.

Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda wani babban jami’in dan sanda na yankin, Larry Leitha ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Tuni dai Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kai dauki yankin na Texas, inda ya ce shi da mai dakinsa Melania na mika sakon jaje da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.

Trump ya kara da cewa jami’an hukumar kashe gobara da sauran jami’an agaji na ta fadi tashin kubutar da al’umma tare kuma da kokarin dakile tasirin ambaliyar.

Baturen ’yan sandan yankin Kerr County, ya sanar da cewa masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane sama da 800 yayin da ake ci gaba laluben kananan yara galibinsu mata da aka nema aka rasa.