Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jajanta wa mutanen da ambaliya da guguwa suka shafa a ƙananan hukumomin Damboa da Askira-Uba.
A cikin kwanakin da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haifar da ambaliya a ƙauyukan Wovi da Gumsuri na Damboa.
- Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
- David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu
Wannan ambaliya ta yi sanadin mutuwar mata biyu, kuma ta lalata gidaje da raba mutane da muhallansu.
A wani ɓangare kuma, guguwa mai ƙarfi ta afka wa garin Rumirgo da ke Askira-Uba, inda ta lalata gidaje da dukiyoyin jama’a.
Dauda Iliya, mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar da sanarwa, inda ya ce abin da ya faru abin tausayi ne da baƙin ciki.
Gwamna Zulum ya ce: “Na yi baƙi ciki da ambaliyar da ta faru a Wovi wadda ta yi sanadin mutuwar mata biyu, da kuma lalata gidaje a Gumsuri.
“Haka kuma abin ya yi muni a Rumirgo inda guguwa ta lalata gidaje. Muna addu’a Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma mayar wa waɗanda suka rasa dukiyarsu da mafificin alheri.”
Gwamnan ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.
Ya kuma tabbatar wa mutanen yankin cewa gwamnati za ta taimaka musu.
Zulum ya ce: “Na riga na umarci hukumar SEMA da ta kai kayan agaji zuwa Gumsuri da Wovi cikin gaggawa. Haka kuma, an riga an tura kayan agaji zuwa Rumirgo.”
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana ƙoƙari wajen daƙile irin wannan iftila’i a gaba, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa kula da bin dokoki don kaucewa irin wannan yanayi.