✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙudan zuma ya tarwatsa ɗaliban da ke jarrabawar NECO

Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira.

Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno.

Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira.

Shaidun gani da ido sun ce, sun ga ɗalibai na barin litattafai da takalma da jakunkuna, har ma da kekunansu yayin da suke gudu daga makarantar.

A cewar wani ɗalibin da ke jarabawar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ƙudan zuman sun daɗe da tarewa a wannan makarantar, amma ba su kai hari a baya ba sai a yanzu.

“Muna rubuta jarrabawar harshen larabci (Arabic) sai ƙudan zuma suka fito gadan-gadan daga wurin da suke da ke harabar makarantar suka far mana da harbi wanda ban san abin da ya jawo harin ba,” in ji wani dalibin.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani harin ƙudan zuma da suka kai a makarantar Shehu Sanda Kyarimi da ke kan titin Bama a birnin na Maiduguri.

Ma’aikatar ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ta jihar Borno ce ke kula da harkokin ilimi a jihar, gami da tabbatar da tsaron makarantu.

Duk da haka, abubuwan da suka faru irin waɗannan suna nuna buƙatar matakan kare ɗalibai daga barazanar da ba zato ba tsammani makamancin abin da ya faru a yanzu.

Harin dai ya kawo cikas ga gudanar da jarabawar NECO cikin kwanciyar hankali, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin ɗalibai da malamai da iyayen wannan makaranta.

Rahoton na nuna cewar, an yi sa’a kawo yanzu ba a samu asarar rayuka ko mummunan jikkata ba.