✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi

A ci gaba da yakin da suke yi da ’yan ta’adda, sojojin Najeriya sun samu nasarar jikkata jagoran kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawy a dajin…

A ci gaba da yakin da suke yi da ’yan ta’adda, sojojin Najeriya sun samu nasarar jikkata jagoran kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi a dajin Sambisa.

Bayanai sun nuna sojoji sun sami nasarar ce bayan wani gagarumin harin da suka kai ta sama a wani sabon sansani na ’yan ta’addan da ke dajin Baikee a yankin Sambisa a Jihar Borno.

Dakarun rundunar da ke karkashin Operation KALACHEN WUTA, wanda bangare ne na rundunar sojojin saman Najeriya da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ne suka kai harin.

Majiyoyin sojojin Najeriya da ke rundunar OPHK wanda Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ke jagorantar ta ce an aiwatar da wannan aiki ne a dajin inda ’yan ta’addan suke ci gaba da taruwa a sabon sansanin da suka kafa tare da shirya kai hare-hare kan fararen hula da ke kusa, musamman garin Izge.

Majiyar ta ce wannan aikin da Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, Kwamandan Rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas a Operation Hadin ke jagoranta, da kuma kwamandan rundunar sojin sama, kwamanda UU Idris, suka shirya a ranar 13 ga watan Yuni 2025 a jere, yadda aka kai hare-hare da dama kan wuraren taruwar ’yan ta’addan, tare da lalata wasu manyan kadarori da kuma kashe manyan kwamandodi na kungiyar ta ISWAP

Kididdigar barnar da majiyoyi suka tabbatar an yi a harin ta tabbatar da cewa kungiyar ta yi mummunar asara.

Wasu majiyoyin leken asiri sun kara tabbatar da cewa fitaccen shugaban kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi, ya samu munanan raunuka a fuskarsa yayin harin ta sama, duk da cewar har yanzu ba a tabbatar da matsayin raunin da ya ji ba.

Nasarar kawar da ’yan ta’addan da kuma wargaza yunkurinsu na sake haduwa ya rage musu karfin fada sannan ya jefa su cikin rudani.