Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara Jihar Neja domin jajanta wa mutanen Mokwa da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa.
Zulum ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 300 domin taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa.
- Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya
- Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3
Zulum, ya ce Gwamnatin Borno ta kawo wannan taimako ne don tallafabwa gwamnatin Neja wajen rage raɗaɗin ambaliyar da ta kashe mutane da lalata dukiyoyi.
Ya kuma buƙaci sauran gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su haɗa kai don kare al’umma daga iftila’i da sauyin yanayi ke haddasawa.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna godiya bisa wannan ziyara da tallafi.
Ya ce ya yi matuƙar farin ciki da irin wannan kulawa da ƙauna da Gwamnatin Borno ta nuna wa al’ummarsa.
Bago, ya tabbatar da cewa za a yi amfani da tallafin cikin gaskiya da adalci, tare da ci gaba da faɗakar da jama’a su guji gina gidaje a kusa da bakin kogi.
Zulum, ya samu rakiyar Sanata Mohammed Tahir Monguno, wasu ‘yan Majalisar Wakilai, Injiniya Bukar Talba, Hon. Abduljadir Rahis da mataimakin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Injiniya Abdullahi Askira.