An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti.
An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.
- Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China
- Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe
Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin yankunan da lamarin ya fi ƙamari, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa na kiwon lafiya.
Kwamishinan lafiya a matakin farko, Dakta Ibrahim Dangana, ya tabbatar da ɓullar cutar, ya kuma ce jihar ta ɗauki matakai da dama domin daƙile yaɗuwar cutar.
A cewarsa, an kafa cibiyoyin kula da lafiya da killace marasa lafiyan a kowace ƙaramar hukumar da abin ya shafa.
Dangana ya ce “Mun kafa cibiyoyin kulawa da killace masu jinya don rage yaɗuwar cutar, kuma muna kuma wayar da kan jama’a kan cutar,” in ji Dangana.
Ya ƙara da cewa, “Shirin wayar da kan jama’a ya shafi Ƙungiyoyin addini irin su Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), kungiyoyin Islama, da masarautu takwas da ke jihar”.
Domin ƙarfafa ƙoƙarin hana yaɗuwar cutar, gwamnatin jihar ta buɗe cibiyar killacewa a tsohon reshen cibiyar kula da lafiya na matakin farko na Marigayi Sanata Idris Ibrahim Kuta daura da tsohon titin filin jirgin sama a Minna.