✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa

Mutane da dama sun shiga fargaba sakamakon aukuwar ambaliyar.

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane da dama tare da lalata gidaje a Ƙananan Hukumomin Yola ta Arewa da ta Yola Kudu a Jihar Adamawa.

Ruwan sama mai ƙarfi da ya fara sauka tun da safiyar ranar Lahadi, ya haifar da ambaliya mai tsanani a sassan birnin.

Yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da Yola Bye Pass, Sabon Pegi, Yolde Pate, da Modire.

Gidaje da dama sun nutse, gonaki sun lalace, hanyoyi kuma sun katse, lamarin da ya hana mutane da ababen hawa zirga-zirga.

Rahotanni sun nuna cewar mutane da dama sun rasu, ciki har da ƙananan yara.

Ya zuwa yanzu ba san adadin waɗanda suka rasu domin hukumomi na ci gaba da aikin ceto.

“Mutane da yawa sun rasu, musamman yara. Har yanzu muna kan aikin neman mutane. Ba mu taɓa tunanin hakan zai faru ba,” in ji Furera Adamu, wata mazauniyar Sabon Pegi.

Aminiya ta gano yankunan Shagari Low Cost da Sabon Pegi sun cika da ruwa gaba maƙil, wanda hakan ya tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu domin neman mafaka a wasu wurare.

Ruwan bai tsaya baya ba har yanzu, wanda hakan zai sa da wuya a iya zama a ciki gidaje a yankin.

Tuni aka yanke wutar lantarki a wasu wuraren da ambaliyar ta fi shafa.

“Muka rasa komai,” in ji wani mazaunin Yola Bye Pass.

“Ruwan ya shigo ta yadda ba mu samu damar ɗebe kayanmu ba.”

Ruwan ya kuma shafe gonaki masu yawa, wanda ya haifar da tsoron za a iya fuskantar ƙarancin abinci a nan gaba.

Maigidanta da dama sun rabu da juna, sannan akwai hatsarin yaɗuwar cututtuka masu nasaba da ruwa sakamakon rashin tsafta a wuraren da ambaliyar ta shafa.

A lokacin haɗa wannan rahoto, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), ba ta fitar da wata sanarwa ba tukuna.

Sai dai Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Adamawa, CP Dankombo Moris, ya tura ‘yan sanda yankin don taimaka wa mutane da ke cikin hatsari.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakaki rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar a ranar Lahadi.

“Ina mai tabbatar muku da cewa rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa tare da haɗin gwiwar sojoji da ke Yola sun tura jami’ai zuwa wuraren da abin ya shafa domin taimaka wa al’umma,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an gano gawarwakin mutum biyu zuwa yanzu, kuma an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama.