Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar PDP.
Atiku, ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023.
- HOTUNA: Atiku, Obi da El-Rufai sun ziyarci kabarin Buhari
- ‘Tinubu ya kamala ayyukan tituna da gadoji sama da 420 a shekara 2’
Ya sanar da hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓar Jada a Jihar Adamawa.
Ɗaya daga cikin hadiman Atiku kan yaɗa labarai, ya tabbatar da sahihancin wasiƙar, wacce aka rubuta a ranar 14 ga watan Yuli, 2025.
A cikin wasiƙar, Atiku ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne saboda jam’iyyar ta kauce daga ƙa’idodin da aka kafa ta.
“Na rubuta wannan wasiƙa ne domin na sanar da ficewata daga jam’iyyar PDP daga yau,” in ji Atiku.
“Ina godiya ƙwarai da dama da goyon bayan da jam’iyyar ta ba ni, musamman kasancewa ta Mataimakin Shugaban Ƙasa na tsawon wa’adin shekaru takwas da kuma tsayawa takarar Shugaban Ƙasa sau biyu a cikinta.
“A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar, wannan mataki dana ɗauka ya sosa min rai sosai,” in shi.
Ya ƙara da cewa: “Amma dole na fice saboda jam’iyyar yanzu ta bi wata hanya da ta saɓa da abin da muka tsaya a kai tun farko.
“Ina rokon Allah Ya taimaki jam’iyyar da shugabanninta a gaba.”
Idan ba a manta ba, Aminiya, ta ruwaito yadda Atiku ya jagoranci wasu jiga-jigan ’yan adawa domin haɗa tafiya mai ƙarfi.
Sun amince da shiga ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita don ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC a zaɓen 2027.