Gwamnatin Tarayya ta ce yanzu haka akwai tituna, gadoji da manyan ayyuka sama da 420 da ko dai ta kammala su ko kuma tana dab da gamawa a shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sanata Barinada Mpigi ne ya sanar da hakan yayin da yake jawabi a taron Hukumar da ke Kula da Ayyukan Injiniyoyi ta Najeriya (COREN) karo na 33 a Abuja ranar Talata.
- DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari
- Akpabio ya daukaka kara kan hukuncin mayar da Natasha kujerarta
Sanatan, wanda Ashley Emenike ya wakilta, ya kuma yaba wa injiniyoyin, wadanda ya bayyana a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin kasa da kuma ayyukan raya kasa.
Ya ce, “A matsayina na shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, dole na tabbatar da cewa injiniyoyi ne ginshikin ci gaban kasa.
“Bisa rahoton ayyukan da yanzu haka ake yi wadanda kwamitina ke aikin sa ido a kansu, mun kiyasta akwai tituna, gadoji da ayyukan raya kasa a fadin Njeriya da wannan gwamnatin ko dai ta kammala su ko kuma saura kiris ta gama su da suka haura 420.
“Daga kan aikin titin Legas zuwa Kalaba zuwa sauran ayyukan titunan da ake yi a bangaren samar da gidaje, makamashi da gadoji a fadin Najeriya, Shugaban Kasa ya nuna aniyar da yake da ita ta ganin Najeriya ta ci gaba,” in ji shi.
Sai dai Sanatan ya nuna damuwa kan yadda ya ce ana yawan samun matsaloli a wasu ayyukan da injiniyoyin ke yi kamar su rushewar gine-gine, lalacewar hanyoyi da sauran ayyuka, inda ya alakanta hakan da rashin bin ka’idojin aiki a lokacin da ake gina su.