Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kaɗu da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a yau, bayan fama da rashin lafiya.
A cikin wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa, Shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa tare da nuna jimami kan rasuwar Buhari.
- Da Ɗumi-ɗumi: Buhari ya rasu a Landan
- Ɗan kasuwar Kano ya yi barazanar maka EFCC a kotu kan zargin ɓata masa suna
Ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Hajiya Aisha Buhari da sauran iyalan mamacin.
Tinubu ya umarci Kashim Shettima, da ya tafi Birtaniya domin dawo da gawar Buhari zuwa gida Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a sauko da tutar Najeriya zuwa rabi a faɗin ƙasar nan domin girmamawa da kuma mutunta tsohon shugaban.
Buhari, ya rasu yana da shekaru 83, ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023.
Kafin nan, ya yi mulki a matsayin shugaban mulkin soja daga watan Janairun 1984 zuwa Agustan 1985, wanda hakan ya sanya shi cikin ƙalilan da suka mulki Najeriya a matsayin soja da kuma farar hula.