Matar tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Zainab Boni Haruna, ta fice daga tsohuwar jam’iyyarta ta PDP zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC.
Zainab, wacce asalinta ta fito ne daga karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe ta bayyana haka ne a wani taro da mata magoya bayan jam’iyyar ta ADC da aka gudanar a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe.
- Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja
- Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda
Zainab Boni ta kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Tinubu kan rashin tsaro, wahalhalu, cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari a kasar nan.
“Mutane suna shan wahala, yunwa ta yi yawa,” in ji ta.
Ta kara da cewa, “Na yanke shawarar shiga jam’iyyar ADC tare da babban wanda na ke karbar shawara kan harkokin siyasa daga wajen shi, Alhaji Adamu Maina Waziri, wanda na yi imanin cewa yana da karfi da dukiya da kuma manufar siyasa don tunkarar APC a zaben 2027.”
Ta kuma ce da yawa daga ’ya’yan jam’iyyar PDP yanzu haka na ficewa suna komawa ADC saboda ba za a iya sasanta rikicin da ke cikin jam’iyyar ba.
“Kafin na yanke shawarar ficewa daga PDP, sai da na je gidan Adamu Waziri wanda tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda ne kuma mamba a kwamitin amintattu na PDP domin neman shawarar siyasa a wurinsa, wadda hakan ne ya bani karfin gwiwar yanke wannan shawarar,” in ji ta.
Sai dai ta bukaci mata da matasan sauran jam’iyyun siyasa da su shirya wa babban zaben shekarar 2027.