✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC

Zulum ya ce yana nan daram a jam'iyyarsa ta APC.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma wata manufa ta ƙashin kansu.

Ya ce yana nan daram a jam’iyyar APC kuma yana biyayya ga jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

Sanarwar ta ce, “Mun ji wani labari da ake yaɗawa cewa zan koma jam’iyyar ADC tare da wasu gwamnoni biyar.

“Wannan labari ba gaskiya ba ne. Waɗanda suka ƙirƙira shi ba sa kishin ƙasa kuma ba sa taimaka wa Jihar Borno ko Nijeriya.”

Zulum ya ƙara da cewa yana nan daram a APC, domin ya damu da ci gaban Jihar Borno.

“Ina roƙon jama’ar Borno da su yi watsi da wannan jita-jita. Mu ba mu da lokacin siyasar da ba ta da amfani. Muna da aiki a gabanmu na ci gaban jiharmu,” in ji shi.

Ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin labarai kafin su yaɗa su.

Hakazalika, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tuƙuru a ƙarƙashin jam’iyyar APC domin ciyar da jihar gaba.