✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno

Sojojin sun kuma daƙile wani harin da ka iya zama wani babban harin da zai haifar da mummunan ɓarnar rayuka da dukiyoyi.

Dakarun rundunar sojin  ‘Operation Haɗin Kai’ sun ce dakarunsu sun kai ga nasarar gano wasu bama-bamai guda 56 da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka binne a kan gadar Marte zuwa Dikwa da ke Jihar Borno.

Sojojin sun kuma daƙile wani harin da ka iya zama wani babban harin da zai haifar da mummunan ɓarnar rayuka da dukiyoyi.

Majiyoyin da ke da alaƙa da rundunar ta OPHK  ta tabbatar da a ranar Juma’a cewa, aka gano bama-baman a wani samame da sojojin na runduna ta 24 da ke Dikwa, Jihar Borno suka yi.

A cewar majiyar, ’yan tada ƙayar bayan sun sanya bama-baman ne a kan gadar da dabarar da nufin yin ɓarna mai yawa tare da daƙile zirga-zirgar sojoji da fararen hula a kan hanyar.

Majiyar ta ce, “Sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun gano na’urorin kafin su tarwatse.

Ya ƙara da cewa, nan take aka tura tawagar da ke kawar da bama-bamai (EOD) zuwa wurin domin taimakawa wajen tabbatar da tsaron na’urorin don kwance su kafin su kaiga tashi.

Hotunan farmakin sun nuna wasu bama-bamai da aka gano a jikin wasu muhimman sassan gadar da ta haɗa manyan garuruwa biyu a Arewacin Borno.

Majiyoyin sun ce saurin shiga tsakani da sojojin suka yi ne ya daƙile wani mummunan harin ta’addanci, wanda ake iya kaiwa jami’an tsaro, al’ummomin farar hula da masu ayyukan jin ƙai a yankin.

Ana ci gaba da sa ido a yankin, yayin da ake ci gaba da aikin share sauran abubuwan fashewa a yankin da zarar an gano su.

Don haka rundunar ta OPHK ke kira ga jama’a musamman masu abubuwan hawa da su riƙa yin taka tsantsan gami da lura akan waɗannan hanyoyin tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an rundunar don magance shi akan lokaci kafin ya kai ga haddasa mummunan lamari.