Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ADC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027.
Sabuwar haɗakar ta haɗa da fitattun ’yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno
- Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa
Sauran sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran shugabannin jam’iyyun adawa.
Sun ƙaddamar da sabuwar haɗakarsu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a ranar Laraba.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, Baba-Ahmed, ya ce wannan matakin da ’yan adawar suka ɗauka yana kama da dabarar da Shugaba Tinubu ya yi kafin zaɓen 2015, lokacin da jam’iyyu suka haɗu suka kafa APC.
Amma ya ce akwai bambanci, domin a 2015, mutane da dama sun riga sun ɗauki Muhammadu Buhari a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tun kafin zaɓen fidda gwani.
Ya ce Tinubu ya goyi bayansa da fatan cewa daga baya zai gaje shi.
Baba-Ahmed ya ce a yanzu, babu wani ɗan takara da aka amince da shi a fili a cikin sabuwar haɗakar.
A cewarsa hakan na iya janyo rikici da gasa mai zafi a lokacin zaɓen fidda gwanin.
“Akwai rashin jituwa a cikin wannan haɗakar. A wancan lokacin, an ɗauki Buhari a matsayin wanda zai yi takara.
“Tinubu ya mara masa baya domin ya san zai zama shugaban ƙasa daga baya. Amma a yanzu, babu wani da aka zaɓa a matsayin ɗan takara.
“Za a samu gasa sosai, kuma wataƙila zaɓen fidda gwani ba zai kasance mai tsafta ba. Tambayar ita ce, me zai faru daga baya?” in ji shi.