✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC

Tsofaffin mukarraban gwamnatin Buhari da suka koma haɗakar ADC sun haɗa da tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni da masu muƙaman siyasa.

Kusoshin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sun shiga haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC da nufin kayar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC.

Tsofaffin mukarraban gwamnatin Buhari da suka koma haɗakar ADC sun haɗa da tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni da masu muƙaman siyasa.

Yawanci sun raba gari da APC ne saboda zargin an yi musu rashin adalci a jam’iyyar da kuma gazawar Gwamnatin Tinubu wajen magance matsalolin da ke ci wa ’yan Najeriya tuwo a ƙwarya.

1- Nasiru El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na gaba ne a tafiyar haɗakar inda tun farko ya lashi takobin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.

Fara maganar haɗakar ke da wuya aka ga El-Rufai a gidan Buhari da ke Kaduna, inda ya sanar da ficewarsa daga APC.

Daga bisani El-Rufai tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da wasu jaga-jigan ’yan APC a gwamnatin Buhari suka ziyarci shugaba kasan.

An yi zargin sun je ne domin neman albarkarsa domin ya amince wa ’yan tsohuwar jam’iyyarsa ta CPC su fice daga APC su shiga haɗakar.

2- Abubakar Malami

Ministan Shari’a a wa’adi biyu da Buhari ya yi, ya sanar da ficewarsa daga APC da kuma aniyarsu ta yaƙar Gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027 saboda ta jefa ’yan Najeriya cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da kuma gaza magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

Tsohon ministan shari’an, kuma wanda tsohon wanda a baya ya nemi takarar Gwamnan Jihar Kebbi, an lura ya yi baya-baya a harkokin APC tun bayan hawan mulkin Tinubu.

3- Rotimi Amaechi

Tsohon Ministan Sufuri a zamanin Buhari, kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta fitowa takarar shugaban ƙasa a ADC.

Amaechi kamar takwarorinsa da suka fice daga APC bisa zargin an yi musu ba daidai ba, na zargin gwamnatin Tinubu da gazawa.

4- Rauf Aregbesola

Tsohon Gwamnan Jihar Osun wanda Buhari ya naɗa Ministan Harkokin Cikin Gida, tsohon na hannun daman Tinubu ne.

A halin yanzu shi ne ADC ta nada a matsayin Sakataren Jam’iyya.

5- Solomon Dalung

Tsohon Ministan Wasanni ya daga cikin waɗanda suka shiga wannan haɗaka ta ADC.

Ko da yake wa’adi daya kadai Dalung ya yi minista a zamanin Buhari, ida gaba bisani ya koma sukan kamun ludayin gwamnatin.

Bayan shafe watanni ana tattaunawa kan haɗakar jam’iyyun adawar ne dai a ranar Laraba suka ƙaddamar da shugabannin riƙo a ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.

Haka kuma sun naɗa tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren riko na ƙasa.