Tsohon Ministan Sufuri, Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da mayar da APC jam’iyyar adawa a Zaɓen 2027.
Yayin wani taron haɗin gwiwar jam’iyyu na adawa a Gombe, an amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasa na bai ɗaya domin fuskantar zaɓen 2027.
- Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC
- NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi
Taron ya gudana a Shugleez Event Centre wanda ya samu halartar fitattun ‘yan adawa daga sassa daban-daban na jihar.
Idris ya ce za su yi haɗakar ce ba wai kawai don karɓar mulki ba, sai dai domin ceton ƙasa da talakawa daga matsin tattalin arziƙi da rashin shugabanci nagari.
Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ya ce jam’iyyar na samun karɓuwa daga sabbin mambobi tare da tabbatar musu da wakilci
Aminiya ta ruwaito cewa an kafa kwamitin rajistar sabbin mambobi ƙarƙashin tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe, John Lazarus Yoriyo, da AVM Adamu Fura a matsayin mataimaki.
Tsohon shugaban matasan APC, Sunusi Abdullahi Ataka, ya ce haɗakar za ta yi tasiri wajen karɓar mulki a Gombe da Najeriya gaba ɗaya.
Wasu daga cikin mahalarta sun haɗa da wakilin Farfesa Isa Ali Pantami, Abubakar Abubakar BD, da sauran jiga-jigai na jam’iyyar ADC.
Bayanai sun ce a yanzu haka jam’iyyar ADC da ’yan haɗaka da wasu jagororin ’yan hamayya suka dunƙule a ƙarƙashin inuwarta ta fara karɓe tsarin jagorancin jam’iyyar PDP a jihohin Yobe da Adamawa da kuma Gombe.
Sun ce an samu ’yan PDP da dama da suka sauya sheƙa zuwa ADC, ciki har da waɗanda suka riƙe manyan muƙamai a baya.
A Jihar Adamawa wasu daga cikin ƙusoshin jam’iyyar da suka riƙe mukamai a matakai daban daban na jiha tuni suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ’yan hadaka ta ADC inda kawo yanzu shugabannin jami’yyar PDP a ƙananan hukumomi goma a cikin jihar suka fice daga cikin jam’iyyar.