Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda hare-haren nan suka rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi.
- Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau
- Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China
Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu.
Ana iya tuna cewa, tun a daren ranar 13 ga watan Yuni zuwa wayewar gari 14 ga watan ne aka kashe fiye da mutum 100 a ƙauyen Yelwata, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar.
Jihar Benuwe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma na ƙabilanci, wanda ke sanadiyyar salwantar rayuka da dama.